[PEN HAUSA] Giwa Ta Faɗi: Magajin Garin Sakkwato Ya Rasu!


Shehu Muhammed Shehu yana rubuta,

Alhaji Hassan Ɗanbaba, magajin garin Sakkwato kuma jika ga Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato ya rasu ne a ranar Assabar 12 ga watan fabrairu, 2022, a garin Kaduna kan hanyar zuwa asibiti bayan ya yanke jiki ya faɗi.

Kamar yanda jaridar The Nation da kuma Dailytrust suka ruwaito, marigayin ya tafi jahar Kaduna ne tun ranar Alhamis domin yin ta'aziya ga tsohon ministan tsaro, Janar Ali Gusau a kan rasuwar ɗan uwansa, inda ya sauka a Otal ɗinsa na Kaduna.

Marigayin ya yanke jiki ne ya faɗi a Otal ɗinsa inda daga nan ne aka ɗauke sa zuwa asibiti, kafin a kai asibiti ne ya ce ga garinku!

Marigayi Alhaji Hassan Ɗanbaba dai ɗa ne ga ɗiyar Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato, wato Aishatu wadda ta rasu shekara ɗaya da ta wuce kuma shi ne shugaban masu naɗa sarki a sarautar Sakkwato.

Kafin rasuwsrsa, shi ne babban daraktan Jarida THISDAY, haka zalika yana ɗaya daga cikin muhimman mutanen da suka haɗu a Legas a makon da ya gabata domin tattaunawa kan yanda za a shawo kan matsalolin da Najeriya ke fama da su gabanin zaben 2023 .

Haka ma, shi ne shugaban hukumar bunƙasa kogin Rima na Sakkwato, waton ( The board of Sokoto Rima river basic development authority).

Marigayin an bayyana shi a matsayin mutum na gari mai son zaman lafiya sannan ga son jama'a da kuma yawan barkwanci.

Alhaji Hassan Ɗanbaba ya rasu yana da shekaru hamsin (50), ya kuma bar mata uku da ƴaƴa shidda. An yi sallar jana'izarsa kamar yadda addinin musulunci ya tanada, sannan kuma aka rufe shi a hubbaren Shehu Usmanu Ɗanfodiyo.

Muhimman mutanen da suka halarce sallar jana'izarsa sun haɗa da : mai martaba sarkin musulmi, Alhaji Sa'adu Abubakar da gwamnonin Kaduna da Kebbi da dai sauransu.

Allah ya gafarta masa ya kuma ba shi Aljannah firdaus. Mu kuma ya kyautata tamu idan ta sallamo.

Post a Comment

0 Comments