PEN HAUSA: Jami'ar Ɗanfodiyo Ce Jami'a Mafi Yawan Farfesoshi a Najeriya — NUC


Shehu Muhammed Shehu ya rubuta,
Hukumar da ke kula da Jami'o'i a Najeriya (NUC) ta bayyana Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo da ke Sakkwato, amatsayin Jami'ar da ta fi kowace Jami'a yawan Farfesoshi a Najeriya.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wani bayani da hukumar ta wallafa a shafinta na yanar gizo, a ranar Larba 29 ga watan Disamba 2021; inda ta bayyana jami'o'in da suka fi yawa da kuma ƙaramcin farfesoshi a Najeriya wanda kuma jaridar PUNCH ta yi sharhi a kansa.
NUC ta ce, ta ɗauki wannan shawara ce domin ana la'akari ne da matakin ƙwarewar malamai wajen auna mizanin nagarta da kuma ingancin Jami'a.
"Wannan wani yunƙuri ne na tantance ingancin malaman Jami'a kuma ƙwarewar malamai a ɓangarora daban-daban shi ne ƙololuwar nagartar Jami'a", NUC ta bayyana.
A cewar hukumar, Jami'ar da ta fi kowace Jami'a yawan Farfesoshi a Najeriya ita ce Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato, wadda ke da kashi 36.44 na Farfesoshi. Yayin da Jami'ar Ubafemi Awolowo, Ile-ife, ta zo ta biyu inda ta ke da kashi 34.80 na Farfesoshi.
Sai kuma Jami'ar Ibadan, da ta zo ta ukku da kashi 29.04; inda Jami'ar Legas kuma aka sanya ta a ƙarƙashin Jami'o'i sha shida da ke da kaso 14. 75 kacal cikin ɗari na Farfesoshi a cikin malamansu
Sauran Jami'o'in gwamnatin tarayya da suke da ƙaramcin kaso su ne: Jami'ar gwamnatin tarayya Oye Ekiti, da Jami'ar gwamnatin tarayya, Lafiya, da Jami'ar aikin gona, Makurɗi, da kuma Jami'ar Umoyo da sauransu.

Post a Comment

0 Comments