Shugaban Sashen Nazarin Harsunan Najeriya Na Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Ya Yi Zama Na Musamman Da Ɗaliban Hausa Domin Farfaɗo Da Ƙungiyar Hausa



Shehu Muhammad Shehu ya karanta,

Dr. Ibrahim Abdullahi Sarkin Sudan, shugaban sashen nazarin harsunan Najeriya na Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato; a jiya jumu'a 3 ga watan Disamba, 2021, ya yi zaman tattaunawa ta musamman da ɗalibai masu nazarin harshen Hausa domin ganin an farfaɗo da ƙungiyar Hausa wadda a shekarun baya ta kasance ƙungiya mafi ƙima da kuma da daraja a Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Ƙungiyar Hausa kamar Yanda aka rubuta a cikin littafi mai ɗauke da dokoki da ƙa'idojin makaranta ( Students Handbook) a shafi na 39, cewa, " ƙungiya ce da kowane ɗalibin Hausa ke da rijista da ita. Sannan ta ƙunshi wasu rukunin ɗalibai masu aikin sa-kai domin ci gaban harshen Hausa ta hanyar gudanar da makon Hausa na shekara-shekara, gabatar da wasannin
kwaikwayo da gasar waƙoƙi rubutattu da kuma na baka da ma sauran ayukan da suka shafi al'adu".

A lokacin zaman, shugaban sashe ya ce, ƙungiyar Hausa ƙungiya ce mai matuƙar muhimmanci wadda kan haɗa kan ɗalibai har ma da malamansu.

A cewarsa, " Mu, a lokacin muna ɗalibai mun ci gajiyar wannan ƙungiyar ƙwarai da gaske, don haka ba za mu bari bakin wuta ya mutu a hannunmu ba, domin idan ƙungiyar na aiki, za a samu haɗin kai da fahimtar juna a tsakanin ɗalibai har ma da malamai.

"Don haka, daga yau, mun naɗa kwamitin riƙon ƙwarya mai muƙamai takawas domin su jogorance wannan ƙungiya kafin a yi zaɓe; kuma muna so su tsara yanda za mu gudanar da taron wayar da kai kafin nan da mako biyu".


Haka ma, shugaban na sashe, ya ja hankalin ɗalibai da su maida hankali ga karatunsu musamman kwasakwasan Gst da na Ingilishi waɗanda su ne ke ci wa ɗaliban Hausa tuwo a ƙwarya.

Farfesa Salisu Ahmad Yakasai, wanda shi ne uban ƙungiyar, a nasa jawabi yayin taron, ya bayyana farin cikinsa a kan taron ya Kuma buƙaci ɗalibai da su zamo masu alfahari da tinƙaho da Hausa a duk inda saka samu kansu domin su kam Hausa ta gama musu komai.

Farfesa Yakasai ya ce, " A gaskiya na yi farin ciki da irin wannan haɗuwa wadda kusan ita ce ta farko a tarihi da ta haɗa fuskokin malamai da ɗalibai wuri ɗaya domin a da, sai ka ga ɗalibai suna nesa-nesa da malamai Kamar za a kama su. Babu abin da ba za ka zama ba, babu abin da ba za ka samu ba kuma babu inda ba za ka je ba da Hausar nan. Gwargwado ba alfahari ba, babu abin da ba mu samu ba kuma babu ƙasashen da ba mu je ba ta dalilin Hausa; wannan ya sa a duk lokacin ni canza mota, sai in sa mata "Bahaushiya ta ɗaya, Bahaushiya ta biyu"... duk domin nuna ta dalilin Hausa na same ta.

"A da, babu wata ƙungiya da take da daraja da ƙima irin wannan ƙungiyar ta Hausa saboda har bobayi za ka ga sun zo suna so a sanya su a ciki, ganin irin tsarin da ake yi na Sarki da Sarauniya". In ji Yakasai.

Bugu da ƙari, Farfesan ya roƙi shugaban sashe da a riƙa sanya irin wannan zama duk bayan mako biyu ko wata ɗaya domin ƙara kawo fahimtar juna a tsakanin malamai da kuma ɗalibai. Ya ƙara da cewa, ƙungiyar Hausa za ta gudanar da gagarumin taro nan gaba, inda za a gayyato manyan sarakunan Hausa domin yin hawan daba a nuna wa duniya cewa har yanzu ƙungiyar tana nan da ƙimarta.

Dr. Yakubu Aliyu Gobir, shi ma yana ɗaya daga cikin maga-isan ƙungiyar, ya yi jan kunne ga ɗalibai da su ƙauracewa duk wani abu da zai zubar musu da ƙima, musamman satar jarabawa da kan iya sa a kore ɗalibi.

Wasu ɗaliban Hausa da PEN PRESS ta zanta da su, sun bayyana farin cikinsu sosai dangane da farfaɗo wa da wannan ƙungiya. Kamar yanda wannan ɗalibin aji biyu mai suna Usama ke cewa, " Gaskiya na ji daɗi sosai domin ban taɓa tunanen akwai irin wannan ƙungiya ba, sai kwatsam! Na ji malamai sun yi kira kowa ya halarce taro za a farfaɗo da Ƙungiyar; gaskiya ba ƙaramin daɗi na ji ba".

Sumayya Yakubu Aliyu, ɗalibar aji uku, ita ma ta bayyana farin cikinta a kan farfaɗo da wannan ƙungiya. " Na ji daɗi sosai da aka ce za a farfaɗo da wannan ƙungiya ganin cewa an ɗauki dogon lokaci wannan ƙungiya ba ta motsi, yanzu kuma ga shi za a farfaɗo da ita". In ji Sumayya.

Daga ƙarshe, shugaban sashe ya karanto sunayen waɗanda aka naɗa domin jagorantar ayukan ƙungiyar kafin a yi zaɓe. Daga ciki waɗanda aka naɗa su ne:

1.Aminu Shehu UGiv, shugaba

2. Abubakar Suleman Ishaq UGll, mataimakin shugaba

3. Musa Abdullahi Maigandu UGlll, sakatare

4. Zulaihatu Adamu UGll, mataimakiyar sakatare

5. Yahaya Abubakar UGlll, Ma'aji

6. Abdul'aziz Abdulƙadir UGl, Sakataren kuɗi

7. Mas'udu Labaran UGIV, kakaki

Ukashatu Haruna UGl, jami'in walwala.

Shugaban na sashe, ya taya su murna sannan ya yi kira a gare su da su kasance masu gaskiya da riƙon amana a yayin gudanar wannan aiki da aka damƙa musu.

Post a Comment

0 Comments